rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Zimbabwe Majalisar Dinkin Duniya Tarayyar Turai Tarayyar Afrika Birtaniya Amurka

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Kasashen duniya sun yi tir da rikicin siyasar Zimbabwe

media
Sojojin Zimbabwe a babban birnin Harare REUTERS/Philimon Bulawayo

Majalisar Dinkin Duniya da Kungiyar Kasashen Turai da Kasashen Birtaniya da Amurka sun bayyana damuwarsu kan halin da ake ciki a Zimbabwe bayan sojoji sun karbe iko da sassan birnin Harare tare da tsare shugaba Robert Mugabe da iyalansa.


Kungiyar Kasashen Afrika ta AU ta yi Allah wadai da abin da ta kira juyin mulkin da aka yi wa shugaban, in da ta bukaci sojojin su koma barikinsu, sannan kuma su mutunta kundin tsarin mulki.

Kungiyar kasashen da ke kudancin Afrika ta SADC ta ce, yau za ta gudanar da taron gaggawa a Botswana domin nazari kan halin da ake ciki.

Shugaban Afrika ta Kudu kuma shugaban kasashen kudancin Afrika Jacob zuma, ya ce, ya yanke shawarar aike wa da jakada don ganawa da shugaban dakarun tsaron da suka aiwatar da wannan aiki, kazalika jakadan zai gana da shugaba Mugabe don fahimtar ainihin abin da ke faruruwa karara a kasar.

A yayin da ake ganin cewa, watakila wannan matakin na sojoji ya yi wa ‘yan adawa dadi, jagoran babbar jam’iyyar adawa ta MDC, Nelson Chamisa cewa ya yi,  za su gana don tabbtar da ainihin abin da ke faruwa da nufin samar da hanyar ci gaban  demokradiya da tsaro da zaman lafiya.

Mai magana da yawun manufofin kasashen ketare ta kungiyar Tarayyar Turai Catherine Ray ta ce, ya kamata a mutunta ‘yancin ‘yan Zimbabwe, sannan kuma a tabbatar da kundin tsarin mulki da gwamnatin demokradiya.

Har yanzu dai sojojin ba su fayyace matsayinsu ba yayin da 'yan kasar ke dakon ganin mataki na gaba da sojojin za su dauka.

Wannan dai na zuwa ne bayan shugaba Mugabe ya kori mataimakinsa Emmerson Mnangwagwa da ke matukar takun saka da uwargidan Mugabe wato Grace Mugabe.

Shugaba Mugabe mai shekaru 93 ya fara jagorancin Zimbabwe ne tun a shekarar 1980 bayan kasar ta samun 'yanci daga turawan Birtaniya, yayin da ake ganin cewa, yana kokarin share wa matarsa fage don darewa kan karagar mulki bayan saukarsa.