Benin
Jami'an kiwon lafiya sun dakatar da yajin aikin watanni biyu da suke yi
A wannan juma’a ma’aikatan kiwon lafiya sun koma a bakin aiki, bayan share tsawon watanni biyu ana yajin aikim da ya yi sanadiyyar tabarbarewar lamurra bangaren kiwon lafiya.
Wallafawa ranar:
Talla
An cimma jituwa tsakanin kungiyar likitoci da gwamnatin kasar a jiya alhamis kamar dai yadda mai magana da yawun kungiyar Adolphe ya tabbatar.
An shiga yajin aikin ne domin neman biyan kudaden alawus da na karin girma ga ma’aikata da dai sauransu, wadanga gwamnatin Patrice Talon ya ce za a gaggata biyan jami’an kiwon lafiyar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu