Isa ga babban shafi
Zimbabwe

Tubabben mataimakin shugaban Zimbabwe ya koma gida

Tubabben mataimakin shugaban kasar Zimbabwe Emmerson Mnangagwa ya koma kasar, mako daya bayan da shugaba Robert Mugabe ya sanar da cewa ya tube daga matsayin, lamarin da shi ne dalilin kutsen soji a fagen siyasar kasar.

Tubabben mataimakin shugaban Zimbabwe, Emmerson Mnangagwa.
Tubabben mataimakin shugaban Zimbabwe, Emmerson Mnangagwa. REUTERS/Philimon Bulawayo
Talla

Wani na hannun daman Emmerson ya tabbatar wa kamfanin dillancin labaran Faransa AFP cewa, jagoran nasu ya koma gida a daidai wannan lokaci da kungiyar kasashen Kudancin Afrika SADC ke kokarin samar da sulhu tsakanin Mugabe da kuma sojojin da ke ci gaba da yi ma sa daurin talala a gidansa.

Bayanai sun tabbatar da cewa Robert Mugabe ya bayyana cewa ba zai sauka daga mukaminsa ba kamar dai yadda sojojin ke bukata, yayin da wasu majiyoyi ke cewa Mugabe na adawa ne da duk wani mataki da zai bai wa Emmerson damar ya gaje shi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.