Isa ga babban shafi
Kenya

'Yan sandan Kenya sun kashe magoya bayan Odinga

Jami’an ‘yan sandan Kenya sun harbe mutane uku har lahira a yayin da magoya bayan jagoran ‘yan adawar kasar Raila Odinga suka yi dandazon tarbar sa a birnin Nairobi.

Dandazon magoya bayan Raila Odinga da suka yi gangamin tarbar sa a filin jiragen sama na Nairobi
Dandazon magoya bayan Raila Odinga da suka yi gangamin tarbar sa a filin jiragen sama na Nairobi AFP
Talla

Wakilin Kamfani Dillancin Labaran Faranaa na AFP, ya ce, ya ga gawarwakin mutane ukun da ‘yan sandan Kenya suka harbe har lahira kwance a tsakiyar titi.

‘Yan sandan sun kuma yi amfani da ruwan zafi da hayaki mai sa kwalla wajen tarwatsa gangamin magoya bayan jagoran ‘yan adawar kasar Raila Odinga, wanda ya dawo daga Amurka a yau Jumma’a.

Gabanin aukuwar wannan lamari, Odinga ya gabatar da jawabi ga magoya bayan nasa jim kadan da saukarsa daga jirgin sama, in da ya ke cewa, "Yau rana ce mai matukar muhimmaci ga siyasar Jamhuriyar Kenya, ina so na mika godiya ga daukacin mutanen Kenya, musamman wadanda suka yi dandazo a filin tashi da saukan jirage don tarba ta".

Sai dai ‘yan sandan sun musanta amfani da harsashin karfe kan magoya bayan Odinga.

Wannan dai na zuwa ne a yayin da ake dakon Kotun Kolin kasar wadda a ranar Litinin mai zuwa za ta yanke hukunci game halascin rantsar da shugaba Uhuru Kenyatta ko akasin haka bayan ya sake samun nasara a zaben da kotun ta bada umarnin sake gudanarwa bayan Odinga ya kalubalanci sakamakon zaben farko a cikin watan Agusta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.