Isa ga babban shafi
Zimbabwe

'Yan Zimbabwe na bikin murnar murkushe mulkin Mugabe

Sojojin Zimbabwe sun dakile dubban masu zanga-zanga a birnin Harare bayan sun yunkurin shiga gidan gwamnatin da shugaba Robert Mugabe ke zama, yayin da ake ci gaba da bikin murnar abin da 'yan kasar suka kira murkushe mulkin Mugabe

Masu zanga-zanga na murnar murkushe shugaban Zimbabwe Robert Mugabe a Harare
Masu zanga-zanga na murnar murkushe shugaban Zimbabwe Robert Mugabe a Harare REUTERS/Philimon Bulawayo
Talla

Masu zanga-zangar da suka yi maci a sassan kasar na bukatar shugaba Mugabe mai shekaru 93 da ya sauka daga karagar mulki bayan sojoji sun karbe ikon tafiyar da kasar daga hannunsa a farkon makon jiya.

Daya daga cikin masu zanga-zangar, Rutendo Maisiri ta shaida wa Kamfanin Dillancin Labaran Faransa na AFP cewa, ba su ji dadin yadda sojojin suka hana su kutsawa cikin gidan gwamnatin ba.

Tun a shekarar 1980 ne shugaba Mugabe ya dare kan karagar mulki bayan samun 'yancin kasar daga hannun Turawan Birtaiya, yayin da 'yan kasar suka kosa da matakan da ya ke dauka musamman kan yadda a baya-bayan ake zargin sa da kokarin taimaka wa uwargidarsa Grace Mugabe wajen darewa kan kujerar mulkin kasar bayan saukarsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.