Isa ga babban shafi
Zimbabwe

Emmerson Mnangagwa ya koma Zimbabwe

Tsohon mataimakin shugaban Zimbabwe da Robert Mugabe mai murabus ya kora makwanni 2 da suka gabata, Emmerson Mnangagwa, ya koma gida yau Laraba, bayan gudun hijirar da ya yi a Afrika ta Kudu.

Emmerson Mnangagwa ya koma birnin Harare
Emmerson Mnangagwa ya koma birnin Harare REUTERS/Mike Hutchings
Talla

Kamfanin dillancin labaran faransa AFP, ya rawaito cewa, tuni Mnangagwa ya gana da jiga-jigan jam’iyya mai mulki ta ZANU-PF, kafin ya wuce masaukinsa.

A ranar Juma’a za a rantsar da Mista Mnangagwa a matsayin shugaban kasar Zimbabwe, bayan kawo karshen mulkinsa na shekaru 37 da Robert Mugabe ya yi a wasikar Murabus da ya rubuta jiya Talata.

Tun a Talatar jami’iyyar ZANU-PF ta amince da Mnangagwa a matsayin wanda zai karashe wa’adin shugabancin Robert Mugabe, har zuwa ranar 28 ga watan Satumba mai zuwa da aka tsayar domin gudanar da zaben kujerar shugabancin kasar.

Zuwa yanzu ana ci gaba da bayyana ra’ayoyi kan irin salon shugabancin da Mnangagwa zai aiwatar, kasancewar yayin da wasu ke murnar Mugabe ya yi Murabus, wasu tasu murnar ragaggiya ce.

Akwai fargabar cewa ba lallai bane a ga sauyin da ake zato, idan aka yi la’akari da biyayyar da Mnangagwan ya yi wa Mugabe a baya.

A shekaru 1980 zuwa da 1989 kungiyoyin kare hakkin dan adam sun zargi Mnangagwa da hannu wajen kashe fararen hula ‘yan adawa akalla 20,000 a lokacin da ya ke shugabancin tsaron cikin gida.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.