Isa ga babban shafi
Zimbabwe

An bai wa Mugabe rigar kariya a Zimbabwe

An bai wa tsohon shugaban Zimbabwe Robert Mugabe rigar kariya da za ta hana shi fuskantar tuhama tare da tabbatar da tsaronsa a kasar.

Tsohon shugaban Zimbabwe Robert Mugabe
Tsohon shugaban Zimbabwe Robert Mugabe REUTERS/Philimon Bulawayo
Talla

Wannan dai na daga cikin yarjejeniyar da aka cimma da tsohon shugaban kafin ya mika takardarsa ta murabus daga kujerarsa kamar yadda wasu majiyoyi gwamnatin suka bayyana a yau ALhamis.

Mugabe ya shaida wa masu shiga tsakani a yarjejeniyar cewa, yana fatan ya mutuwa ta riske shi a Zimbabwe kuma ba shi da burin rayuwa a kasar waje.

A ranar Talatar da ta gabata ne, Mugabe mai shekaru 93 ya sauka daga kujerar mulkin wanda ya dare tun a shekarar 1980 , lokacin da kasar ta samu ‘yanci daga Turawan Birtaniya.

Sojojin kasar sun taka rawa wajen kawo karshen mulkin Mugabe, yayin da jam’iyyarsa ta ZANU-PF ta juya ma sa baya.

Yanzu haka dai ana shirin rantsar da Emmerson Mnangagwa a gobe Jumma’a a matsayin shugaban kasar Zimbabwe na rikon kwarya bayan Mugabe ya sauke shi daga mukaminsa na mataimakin shugaban kasa sama da makwanni biyu da suka gabata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.