rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Zimbabwe Uganda Congo Brazaville Jamhuriyar Demokradiyyar Congo Togo Kamaru

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Makomar shugabannin Afrika bayan saukar Mugabe

media
Tsohon shugaban Zimbabwe Robert Mugabe ALEXANDER JOE / AFP

Bayan wasu sa’oi da tilasta wa Robert Mugabe yin murabus daga karagar mulkin Zimbabwe, yanzu haka shugabannin Afrika da suka dade kan karaga na nazari game da makomarsu, abin da ya sa wasunsu suka fara bullo da tsare-tsaren kyautata wa jama’a.


Ana ganin matsin lambar da Robert Mugabe ya sha har ya yi murabus daga kujerarsa, ya tilasta wa shugabannin kasashen Afrika da suka dade kan karagar mulki daukan wasu matakai na dadada wa mutanen kasarsu.

Shugaban Uganda Yoweri Museveni da ya shafe shekaru 31 akan karaga ya aika da wani sakon Tweeter, in da ya bayyana shirinsa na karin albashi ga ma’aikatan gwamnati da kuma inganta tarin aikin sojin kasar.

Masharhanta na ganin cewa, rashin tabbas ne game da makomar kujerarsa ya sanya Museveni mai shekaru 73 bullo da sabbin tsare-tasren.

Sauran shugabannin na Afrika da suka dade kan karagar mulki sun hada da Teodoro Obiang na Guinea da ya shafe shekaru 38 da kuma Paul Biya na Kamaru da ya shafe shekaru 35, sai kuma Denis Sassou Nguesso da ya yi mulkin shekaru 33 a Congo.

Suma dai iyakan gidan Gnassingbe Eyadema na Togo sun dauki shekaru 50 suna mulki a kasar, in da a Jamhuiyar Demokradiyar Congo, iyalan gidan Kabila suka fara jagoaranci kasar tun daga shekarar 1997.

Masharhanta na ganin cewa, nan kusa dai, karshen mulkiin wadandan shugabannin zai kawo karshe musamman ma idan aka yi la’akari da irin matakan da suke dauka na murkushe ‘yan adawa da kuma tabarbarewar tattalin arzikinsu.

A farkon wannan makon ne, Robert Mugabe na Zimbabwe ya sha matsin lamba daga sojoji da al’ummar kasar har sai da ya sauka daga mulki bayan shafe shekaru 37.