rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Zimbabwe Robert Mugabe

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

An rantsar da sabon Shugaban Zimbabwe

media
Emmerson Mnangagwa tareda matarsa sun iso filin wasa na birnin Harare Marco Longari / AFP

A yau juma’a aka rantsar da Emmerson Mnangagwa a matsayin shugaban kasar Zimbabwe, bayan kawo karshen mulkin Robert Mugabe na tsawon shekaru 37.


An yi bikin rantsar da Mnangagwa a filin wasa da ke babban birnin kasar Harare, bayan dawowarsa gida a ranar Laraba, daga gudun hijirar da ya yi zuwa Afrika ta Kudu, sakamakon korar shi daga mukamin mataimakin shugaban kasa da Mugabe ya yi a farkon watan da muke ciki.

Korar da Mugabe ya yi Mnangagwa, ta taka rawa wajen sanya jam’iyya, mai mulkin kasar ZANU-PF da kuma rundunar sojojin kasar yin ruwa da tsaki wajen kawo karshen rudanin siyasar kasar, bayan da Mugabe ya rubuta takardar Murabus.