Isa ga babban shafi
Rwanda-Libya

Rwanda zata bai wa Bakin-haure mafaka

Gwamnatin Rwanda ta yi tayin bada mafaka ga bakin-hauren nahiyar Afrika akalla dubu 30,000 da ke fuskantar cin zarafi a Libya bayan tsaresu da aka yi sansanoni daban daban da ke kasar.

Des migrants sauvés par les gardes côtes de Tripoli, le 6 novembre 2017.
Des migrants sauvés par les gardes côtes de Tripoli, le 6 novembre 2017. REUTERS/Ahmed Jadallah
Talla

Bayan kasar Burkina Faso da ta janye jakadan ta da Libya,tayin kasar Rwanda na zuwa yayin da kasashen Duniya ke ci gaba da allah wadai kan halin da bakin hauren suka samu kan su a kasar ta Libya.

Kan haka ne kuma kungiyar kasashen Afrika ta AU ke tuntunbar shugabanin yankin da na Turai don ganin an kawo karshen batun sayar da bayi da ake zargin wasu yan kasar ta Libya da aikatawa.

Moussa Fakir, Shugaban hukumar zartarwa ta kungiyar AU ya bukaci sauran kasashen nahiyar su bada a hadin kai don kawo karshen cinikin bayi a kasar ta Libya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.