Isa ga babban shafi
Libya

'Yan-cirani 25 sun mutu bayan nutsewa a tekun Libya

Akalla ‘yan cirani 25 ne suka mutu sakamakon nutsewar da jirginsu ya yi a gabar tekun Libya yau Asabar .Jami’an hukumar da ke kula da tsaron Tekun sun ce an kuma ceto mutane da dama kafin su kai ga halaka, lamarin da ya sa aka mayar da su tashar jirgin da suka ta so.

A cewar hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta duniya, fiye da ‘yan-cirani dubu 3 ne suka mutu ko kuma suka bace cikin shekarar nan a kokarinsu na tsallaka Nahiyar Turai daga Libya.
A cewar hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta duniya, fiye da ‘yan-cirani dubu 3 ne suka mutu ko kuma suka bace cikin shekarar nan a kokarinsu na tsallaka Nahiyar Turai daga Libya. REUTERS/Ahmed Jadallah
Talla

Libya dai ita ce hanya mafi sauki da bakin haure kan yi amfani da ita wajen tsallakawa nahiyar Turai, sai dai da dama daga cikin masu wannan yunkuri kan gamu da matsaloli.

haka zalika masu safarar mutane kan yi amfani da damar wajen kwashe mutanen ko kuma galibi a sanya su lalataccen jirgin da zai karye ko kuma ya nutse suna tsaka da tafiya.

A bangare guda kuma manyan jirage kan kwashi bakin hauren don dangana su da Italiya, kasar da yanzu haka ke koka yawan bakin hauren da ke zaune cikin ta, inda akalla ta ke da yawan ‘yan ci rani fiye da dubu dari da sha biyar.

A cewar hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta duniya, fiye da ‘yan-cirani dubu 3 ne suka mutu ko kuma suka bace cikin shekarar nan a kokarinsu na tsallaka Nahiyar Turai daga Libya.

hukumar ta ce tun bayan shekarar 2000 tekun Maditerranean ya zamo wata babbar hanyar lakume rayukan jama’a.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.