Isa ga babban shafi
Faransa

Emmanuel Macron ya fara ziyara a Afirka

Shugaban Kasar Faransa Emmanuel Macron ya fara ziyarar wasu kasashen Afirka inda ake saran zai bunkasa karfin fada ajin kasar a nahiyar da kuma karfafa matasan da ke fatan zuwa Turai cewar zasu fi samun rayuwa mai inganci a kasashen su.

Shugaba Emmanuel Macron na Faransa
Shugaba Emmanuel Macron na Faransa LUDOVIC MARIN / AFP
Talla

Ziyarar shugaba Emmanuel Macron zata fara ne da kasashen Burkina Faso da Cote d’Ivoire, biyu daga cikn kasashen da kasar ta yiwa mulkin mallaka, sai kuma kasar Ghana.

Ziyarar na zuwa ne a dai-dai lokacin da kasashen Turai ke kokarin kawo karshen yadda matasa daga Afirka ke kwarara zuwa Turai domin samun rayuwa mai inganci, inda da dama daga cikin su ke mutuwa a teku, ko kuma fadawa hannun 'yan bindiga a Libya wadanda ke sayar da su a matsayin bayi.

Ana saran shugaban ya nemi goyan bayan kasashen Afirka kan sabuwar rundunar da aka girka a yankin Sahel domin yaki da 'yan ta’adda, wadda Faransa ke fatar ganin ta yi karfi domin janye dakarun ta daga kasar.

Ana kuma saran shugaban ya nemi hadin kai wajen bunkasa ilimi da kuma horar da matasa sana’o'i.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.