Isa ga babban shafi
Najeriya

Buhari ya fice zuwa Abidjan domin taron AU-EU

Taron na shugabannin kasahen nahiyar Afirka da Turai zai tattauna ne a kan batutuwa da suka hada da tattalin arziki, da tsaro, da kuma magance matsalar kwararar baki da sauransu.

Taron na kasashen Afirka da Turai zai gudana ne a garin Abidjan.
Taron na kasashen Afirka da Turai zai gudana ne a garin Abidjan. RFIHausa/Kabiru Yusuf
Talla

A ranar Laraba da Alhamis ne ake sa ran shugabannin kasashen za su daddale kan al'amuran da suka fi shafar bangarorin guda biyu.

Ana sa ran shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai tattauna da shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron a gefen taron, inda za su tattauna a kan dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu.

To sai dai gamayyar kungiyoyin fararen hular nahiyar Afirka da ake kira 'Tournons la Page' na kallon taron na Abidjan a matsayin wata haduwa domin kare muradun kasashen Turai kawai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.