rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Sudan Darfur

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Dakarun Sudan sun kama daya daga cikin shugabanin yan tawayen Darfur

media
Omar al-Bashir Shugaban Sudan REUTERS/Mohamed Nureldin Abdallah

Hukumomin kasar Sudan sun ce jami’an tsaro sun yi nasarar kama daya daga cikin shugabanin yan tawayen Darfur da Majalisar Dinkin Duniya ta zarga da cin zarafin jama’a.


Jami’an tsaro sun kama Musa Hilal, tsohon hadimin shugaba Omar Hassan al Bashir, kusa da garin su dake Mustariaha a arewacin Darfur.

Ministan tsaro Ali Mohammed Salem ya ce bayan Hilal an kuma kama dan sa wadanda ake tsare da su yanzu haka.