Isa ga babban shafi
Mali

Gwamnatin Mali ta dage zaben kananan hukumomi

Gwamnatin kasar Mali ta sanar da jinkirta zabukan kananan hukumomi, saboda matsalar rashin kwanciyar hankali, sakamakon tashin hankalin da ake samu a sassan kasar.

Shugaban kasar Mali Ibrahim Boubacar Keita a lokacin da ya ke kada kuri'a a birnin Bamako, yayin zaben kananan hukumomi, a ranar 20 ga watan Nuwamba, 2016.
Shugaban kasar Mali Ibrahim Boubacar Keita a lokacin da ya ke kada kuri'a a birnin Bamako, yayin zaben kananan hukumomi, a ranar 20 ga watan Nuwamba, 2016. Habibou Kouyate / AFP
Talla

Aboubacar Sidick Fomba, shugaban hukumar zaben, yace an dage zaben kananan hukumomin daga watan Disamba zuwa Afrilu na shekara mai zuwa.

Tashe tashen hankulan da ake samu sun yi sanadiyar hallaka sojojin Majalisar Dinkin Duniya 4 da na Mali guda da kuma jikkata wasu 21.

A ranar Asabar da ta gabata, hukumomin tsaron Mali suka tabbatar da mutuwar dakarun wanzar da zaman lafiyar 4 sakamakon harin da ‘yan tawaye suka musu a yankin Menaka da ke arewa maso gabashin kasar.

Sai dai rundunar ta MINUSMA ta ce dakarunta sun hallaka mayakan ‘yan tawayen da dama, a martanin da suka mai da.

A ranar 26 ga watan Oktoban da ya gabata, sai da ‘yan tawayen na Mali suka hallaka wasu dakarun rundunar ta MINUSMA 4, da suka fito daga Chadi, bayan da motar su ta taka nakiyar da aka dasa musu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.