Isa ga babban shafi
Kenya

Uhuru Kenyatta ya karbi rantsuwar shugabanci wa'adi na 2

Uhuru Kenyatta ya karbi rantsuwar fara aiki a matsayin shugaban kasar Kenya, a wa’adinsa na karshe da zai shafe shekaru 5.

Shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta yayin karbar rantsuwar fara aiki a birnin Nairobi, wa'adi na biyu. 28 ga Nuwamba, 2017.
Shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta yayin karbar rantsuwar fara aiki a birnin Nairobi, wa'adi na biyu. 28 ga Nuwamba, 2017. REUTERS/Thomas Mukoya
Talla

Akalla mutane dubu 60,000 ne suka halarci bikin rantsuwar a filin wasa na Kasarani da ke birnin Nairobi.

Daga cikin shugabanni ko wakilan kasashen Afrika da suka halarci bikin rantsuwar akwai, Sudan ta Kudu, Uganda, Rwanda, Zambia da kuma Somalia.

Sai dai, yayin da ake shirin fara bikin rantsuwar, sai da jami’an tsaro, suka yi amfani da hayaki mai sa hawaye kan wasu magoya bayan jagoran ‘yan adawa Raila Odinga, da suka yi yunkurin gudanar da zanga-zanga, wadda suka ce sun shirya ta ne, domin tunawa da mutanen da suka rasa rayukansu a tashin hankalin da ya biyo bayan jerin zanga-zanga da arrangamar da suka yi da ‘yan sanda, dalilin nuna adawa da sakamakon zaben, da ya bai wa Uhuru Kenyatta damar sake darewa kujerar shugabancin kasar wa'adi na 2.

Bikin rantsuwar ya zo ne bayan da kotun kolin kasar, ta tabbatar da nasarar Kenyatta a ranar Litinin ta makon da ya gabata, bayan da a baya, ta soke zaben shugabancin da aka yi a watan Agusta sakamakon korafin 'yan adawa na cewa a tafka magudi.

A watan Oktoba Uhuru Kenyatta ya sake lashe zaben da kotun ta bada umarnin shiryawa da akalla kashi 54 na kuri'un da aka kada.

Kamfanin dillacin labarai na AFP, ya ce bayan fara samun rikicin siyasa a dalilin zaben shugabancin kasar na wannan shekara a watan Agusta, mutane 56 ne suka mutu zuwa yanzu, kuma kungiyoyi sun bayyana cewa akasarin wadanda suka rasa rayukansu, ‘yan sandan kasar ne suka hallaka su.

Hukuncin kotun kolin kasar na amincewa da zaben da aka sake yi wa Kenyata, ya raba kawunan al’ummar kasar, wanda a cikin wannan yanayi ne shugaba Kenyatta ya karbi rantsuwar kama aiki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.