Isa ga babban shafi
Kamaru

'Yan aware sun kashe sojojin Kamaru

Rundunar sojin kamaru ta ce wasu da ta ke zargin ‘yan aware ne, sun kashe jami’anta 4, a wani yankin masu amfani da harshen turancin Ingilishi.

Jami'an tsaron jamhuriyar Kamaru.
Jami'an tsaron jamhuriyar Kamaru. STRINGER / AFP
Talla

Kisan jami’an tsaron da ‘yan awaren suka yi ya nuna yadda sha’anin tsaro ke kara tabarbarewa a yankunan kudu-maso-yammaci, da kuma arewa-maso-yammacin kasar, inda ake da rinjayen masu amfani da harshen Ingilishi.

A cikin watan Nuwamba kadai, jami’an tsaron Kamaru 8 mahara da ake zargin ‘yan aware ne suka hallaka.

‘Yan awaren suna zargin gwamnatin Paul Biya da nuna wa yankunan su wariya, musamman a fannonin da suka shafi Ilimi, tattalin arziki da kuma rashin damawa da su a harkokin tafiyar da kasar.

A ranar 10 ga watan Nuwamba ne gwamnati ta kafa dokar hana zirga-zirga a yankunan masu amfani da Ingilishi domin abinda ta kira kokarin dakile barazanar tsaron.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.