Isa ga babban shafi
Sudan ta Kudu

Rikicin Kabilanci ya lakume rayuka 50 a Sudan ta Kudu

Akalla mutum 50 ‘yan bindiga suka kashe a gabashin Sudan ta Kudu, harin da ke kasance irinsa na baya-bayanan da ake fuskanta a yankin da ake yawaita samun rikicin kabilanci.

Rikicin kabilanci na lakume rayuka a Suda ta Kudu
Rikicin kabilanci na lakume rayuka a Suda ta Kudu REUTERS/Goran Tomasevic
Talla

A cewar wani karamin Minista, Dut Achuek, an kashe Mutum 8 a harin farko da aka kai ranar Litinni a jihar Jonglei, sai kuma jiya aka sake hallaka mata 23 da maza 19.

Akasarin wadanda harin ya ritsa dasu fararren hula ne, wanda aka kona musu gidaje da sace dukiyoyinsu.

‘Yan bindigan Murle ne suka kaddamar da hari kan kabilar Dinkas da ke rayuwa a wani kauye mai nisan kilimita 150 da arewacin Bor.

Ministan yada labaran a jahar Boma, Kudumoc Nyakurono, da ke tabbatar da harin, ya ce an kaddamar da binciken sa ni hakikanin abin da ya auku.

An jima ana samun Rikicin kabilanci tsakanin mutanen da ke rayuwa a kudanci Sudan, satar dabobbi da kayayaki da aikata fyade kan mata da garkuwa da kananan yara, lamarin da ke tursasa ramako.

A shekara ta 2012 an samu kazamin rikici tsakanin kabilun, wanda ya yi sanadi mutuwar mutum sama da dubu 3.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.