Isa ga babban shafi
Najeriya

Harin kunar bakin wake ya hallaka mutum 13 a Borno

Wasu da ake kyautata zaton mayakan kungiyar boko haram sun kaddamar da wani harin kunar bakin wake a garin Biu na jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya wanda ya hallaka akalla mutum 13 baya ga jikkata da dama.

Harin ya faru ne a dai dai lokacin da mabukata ke tsaka da karbar agajin abinci.
Harin ya faru ne a dai dai lokacin da mabukata ke tsaka da karbar agajin abinci. STRINGER / AFP
Talla

Kakakin ‘yan sandan jihar Borno Victor Isiku ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce yanzu haka akwai mutum 53 wadanda ke karbar kulawar gaggawa sanadiyyar harin baya ga mutum 13 da suka mutu.

Lamarin dai a cewar rundunar ‘yan sanda ya faru ne a wata kasuwa da ke cikin garin na Biu lokacin da ake tsaka da rabawa wasu mabukata abinci a yau asabar.

Harin na yau Asabar na zuwa ne a dai dai lokacin da rundunar sojin kasar ke cewa ta hallaka mayakan kungiyar ta Boko Haram 3 a kauyen Gajibo cikin karamar hukumar Dikwa a jihar Borno.

A baya bayan nan dai kungiyar ta Boko Haram ta kaddamar da munana hare-hare a sassan kasar ciki har da na masallacin juma'a a jihar Adamawa da ya hallaka fiye da mutum 50.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.