rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Amurka Birtaniya Najeriya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Birtaniya da Amurka sun yi gargadin faruwar hare-hare a Najeriya

media
A baya bayan nan kungiyar Boko Haram ta tsananta kai hare-hare wasu sassan Najeriya musamman yankin arewa maso gabashin kasar. © AFP PHOTO / BOKO HARAM

Kasashen Amurka da Birtaniya sun yi gargadin cewa ‘Yan ta’adda na shirye-shirye kaddamar da muggan hare-hare yayin bukukuwan Kirsimeti a Abuja babban birnin Najeriya.


Sanarwar da Ofishin kula da harkokin ‘yan Birtaniya a Najeriya ya fitar ya ce za su ci gaba da bibiya don gano shirye-shiryen ‘yan ta’addan musamman a wannan lokaci na bukukuwan Kirsimeti.

Tuni dai Birtaniyar ta fitar da sanarwar cewa dole ne al’ummar fiye da dubu 117 da ke shiga Najeriyar kowacce shekara su kauracewa zuwa wuraren ibadu da kasuwanni da wuraren shakatawa ko sansanin ‘yan gudun hijira a kasar.

A bangare guda kuma Amurka ta gargadi al’ummarta da su kaucewa ziyartar jihohin Adamawa da Bauchi da Borno da Gombe da Jigawa da kuma Yobe har zuwa lokacin da za a kammala bukukuwan Kirsimeti da sabuwar shekara.

Duk da ikirarin da gwamnatin kasar ke yi na fatattakar Mayakan kungiyar Boko haram, har yanzu Najeriyar na fuskanta hare-haren kungiyar wanda ke sabbaba asarar rayukan jama'a.

Ko a makon da ya gabata sai da mayakan suka hallaka fiye da mutum 50 a wani masallacin juma'a da ke Adamawa yayin da a bangare guda kuma wani harin kunar bakin wake a jiya Asabar ya hallaka fiye da mutum 15.