Isa ga babban shafi

Siyasar Togo: 'Yan adawa sun sha alwashin ci gaba da zanga-zanga

Dubban ‘yan kasar Togo sun sake gudanar da zanga-zanga a birnin Lome, karo na uku cikin wannan makon, domin tilastawa shugaban kasar Faure Gnassingbé ya sauka daga mukaminsa.

Shugaban kasar Togo, Faure Gnassingbé.
Shugaban kasar Togo, Faure Gnassingbé. REUTERS/Luc Gnago
Talla

Zanga-zangar ta zo a dai dai lokacin da shugaban Ghana nana Akufo Addo da takwaransa na Guinea Alpha Conde, kokarin shiga tsakanin bangaren gwamnati da na ‘yan adawar kasar.

A watan Nuwamban da ya gabata ne Shugaba Gnassingbé, da ya shafe shekaru 15 yana jagorancin Togo, ya yi alkawarin zai tattaunawa da ‘yan adawa, sai dai har yanzu bai ce komai ba kan alkawarin, lamarin da ya fusata jam’iyyun adawar kasar.

Yayin zantawa da kamfanin dillancin labaran Faransa AFP, jagoran jam’iyyar adawa ta NAC, ya ce ba zasu daina zanga-zangar ba har sai shugaba Faure Gnassingbe ya sauka daga mukaminsa.

Tun a watan Agustan da ya gabata, jam’iyyun adawar Togo guda 14, suka kaddamar da zanga-zangar, wadanda kuma suka ce zasu amince da fara tattaunawa da gwamnati ne idan ta cika sharadin da suka gindaya mata, na sakin daruruwan ‘yan adawar da ta tsare.

Zalika sun kuma bukaci gwamnatin kasar, da ta dage haramcin gudanar da zanga-zangar da ta sanya, tare da mayar da sojoji zuwa barikokinsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.