rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Jamhuriyar Demokradiyyar Congo Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres Tanzania

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

'Yan bindiga sun kashe dakarun wanzar da zaman lafiya a Congo

media
Dakarun wanzar da tsaro na majalisar dinkin duniya a DRC. cfr.org

Akalla dakarun wanzar da zaman lafiya na majalisar dinkin duniya guda 14 da sojojin Congo guda 5 ne wasu da ake zargin 'yan bindiga ne suka hallaka sakamakon wani hari da suka kai a wani sansani da ke gabashin kasar Congo.


Sakatare-janar na majalisar dinkin duniya Antonio Giuterres ya ce rahotanni da aka fara samu sun nuna cewa dakaru guda 14 da suka fito daga kasar Tanzania ne aka kashe a yammacin ranar Alhamis a arewacin Kivu da ke gabashin Congo.

Wasu dakarun guda 53 ne aka raunata, yayin da 4 daga cikinsu ke cikin mawuyacin hali.

A cikin sanarwar da ya fitar, Antonio Guterres ya bayyana al’amarin a matsayin laifin yaki wanda ba za a amince da shi ba.

Ya kuma yi kira ga kasar ta jamhuriyar demokradiyyar Congo da ta yi bincike sannan ta hukunta wadanda suka aikata kisan.