rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Cutar Sida Tarayyar Afrika

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Cutar Sida a Afirka

media
Taron Mahiyar Afirka dangane da cutar Sida a Abidjan ©icasa2017cotedivoire.org

An kawo karshen babban taro karo na 19 a Abidjan na kasar Cote D’Ivoire dangane da cutar Sida dama hanyoyin kawar da kamuwa da ita a Afrika.


Taron ya samu halartar masana dama likitoci ya kuma mayar da hankali dama karfafa hanyoyi fadakar da al’uma domin kare kai, tareda yi kira zuwa kungiyoyi na ganin sun maida hankali zuwa mata yan kasa da shekaru 20 dake dauke da kwayar cutar Sida, da mata masu juna biyu a nahiyar ta Afirka.

Mahalarta taron suna san ran ganin an kawo karshen wannan cuta nan da shekara ta 2030,sun kuma bayyana cewa samun wannan nasara sai da hadin kan Shuwagabani, kungiyoyi masu zaman kan su da ma kungiyar nahiyar Afirka .