Isa ga babban shafi
Sudan ta Kudu

Sudan ta Kudu na bukatar agajin $1.7 a 2018

Majalisar Dinkin Duniya da gwamnatin Sudan ta Kudu sun ce kasar na bukatar agajin akalla dala biliyan 1.7 a shekara mai kamawa domin taimakawa kusan rabin al’ummarta da suka fada matsanancin talauci da yunwa sakamakon yakin da kasar ta tsunduma tsawon shekaru.

Iyalai na cikin yunwa a Sudan ta Kudu
Iyalai na cikin yunwa a Sudan ta Kudu Thomson Reuters Foundation/Stefanie Glinski\n
Talla

Sanarwar da bangarorin biyu suka fitar, ta nuna cewa akwai fiye da mutum milyan 6 da ke cikin matsanancin hali a kasar sakamakon yakin da ya jefa su cikin talauci da yunwa.

A cewar babban jami’i mai kula da ayyukan jin-kai na Majalisar a kasar, Alain Noudehou, za su yi amfani da dala biliyan daya da miliyan dari bakwai wajen tallafawa mutum miliyan shida da ke tsananin bukatar agaji a kasar, wadanda galibinsu sun rasa muhallinsu.

Tun bayan samun ‘yancin kasar ta Sudan ta kudu mai yawan jama’a miliyan 12 a shekarar 2013, kasar ta tsunduma cikin yakin basasan da ya tilastawa kusan kaso daya bisa Ukun al’ummarta ficewa daga kasar.

Yakin kasar ya fara ne tsakanin bangaren shugaba Salva Kiir da tsohon mataimakinsa Riek Machar da yanzu ke kasar Afrika ta kudu bayan zargin yunkurin juyin mulki, kafin daga bisani ya koma fadan kabilanci tsakanin al’ummar kasar wanda ke ci gaba da sabbaba asarar rayuka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.