Isa ga babban shafi
Chadi

Amurka ta tura da tawaga zuwa kasar Chadi

Tawagar kasar Amurka da ta gana da mahukunta kasar Chadi kan batun takunkumin hana 'yan kasar tafiya kasar Amurka, ta bukaci mahukuntan kasar da su gaggauta karin inganta harkan tsaro, musamman takardun tafiya wato Passport kafin kasar Amurka ta gamsu ta dage takunkumin da ta sanya wa kasar.

Idriss Déby, Shugaban kasar Chadi
Idriss Déby, Shugaban kasar Chadi REUTERS
Talla

Shugaban Amurka Donald Trump ya sanya kasar Chadi cikin kasashe 8 da aka haramtawa ‘Yan kasar shiga Amurka saboda abinda ya kira matsalar tsaro da kuma rashin ba Amurka hadin kan da ya dace.

Shugaba Trump ya ce ya dauki matakin ne domin kare lafiyar Amurkawa daga hare hare. Sauran sabbin kasashen da aka bayyana sunayensu sun hada da Koriya ta Arewa da Venezuela.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.