rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Zimbabwe Emmerson Mnangagwa

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

ZANU-PF ta tsayar da Mnangagwa a Matsayin dan takararta

media
Shugaban Zimbabwe Emmerson Mnangagwa REUTERS/Philimon Bulaway

Jam’iyyar ZANU-PF a Zimbabwe ta tsayar da shugaban kasar mai-ci Emmerson Mnangagwa a matsayin wanda zai tsaya mata takarar shugabancin kasa a zaben kasar da za a gudanar cikin shekara mai zuwa.


A watan da ya gabata Mnangagwa ya dare karagar mulkin kasar bayan sojoji sun tilastawa shugaba Robert Mugabe yin Murabus, wanda kuma jam’iyyar ZANU-PF ta taka muhimmiyar rawa kan lamarin.

Gabanin taron Jam'iyyar yau juma'a, Mista Mnangagwa ya bukaci Jam’iyyar sa ta ZANU PF da ta tababtar an gudanar da karbaben zaben da kowa zai amince da shi.

Shugaban ya ce duniya ta zuba ido ta ga yadda zaben zai gudana da zummar kulla wata sabuwar dangataka da kasar.