rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Africa ta kudu Jacob Zuma

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Jam'iyyar ANC ta zabi sabon shugaba

media
Jam'iyyar ANC ta zabi Cyril Ramaphosa a matsayin sabon shugabanta REUTERS/Siphiwe Sibeko

Magoya bayan jam’iyyar ANC, sun zabi mataimakin shugaban kasar Cyril Ramaphosa a matsayin shugaban jam’iyyar, inda ya samu kuri’u 2,440, a gaban abokiyar hamayyarsa tsohuwar matar Jacob Zuma Nkosazana Dlamini-Zuma wadda ta samu kuri’u 2,261.


Wannan dai nasara ce da ke share wa Ramaphosa fage domin darewa kan karagar shugabancin kasar a zaben da za a yi shekara ta 2019 bayan kawo karshen wa’adin shugabancin Jacob Zuma.

A lokacin da aka sanar da sakamakon, dimbin magoya bayan mataimakin shugaban kasar da ke cikin zauren taron ne suka kece da ihu domin murna.

To sai dai tun kafin fitar da sakamakon zaben ne magoya bayan Dlamini-Zuma suka fara zargin cewa za a tafka magudi, musamman lura da irin matakan da aka dauka domin hana wasu daruruwa daga cikinsu damar kada kuri’unsu.