rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Kamaru Tarayyar Afrika

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Ƙasashe renon Ingila sun gargaɗi Kamaru

media
Yankin masu amfani da hashen Ingilishi a Kamaru ya dade yana fama da tashin hankali. AFP

Shugabar ƙungiyar ƙasashe renon Ingila, Patricia Scotland ta buƙaci Kamaru da ta bi matakin tattaunawa da ƴan awaren ƙasar da ke yankin da ake amfani da turancin Ingilishi domin kawo ƙarshen rikicin da ake samu a yankin.


Scotland wadda ke ziyarar kwanaki 4 a ƙasar Kamaru ta bayyana takaicin ta da tashe-tashen hankulan da ke faruwa a yankin Arewa-maso-Yamma da kuma Kudu-maso-Yammacin ƙasar.

Jami’ar ta ce an san Kamaru da zaman lafiya, saboda haka ya zama wajibi al’ummar ƙasar su kawar da banbance-banbancen da ke tsakanin su domin magance matsalar da ake fama da ita.

Masu amafani da harshen Ingilishi a Kamaru, waɗanda ke da kashi 20 cikin ɗari na yawan al'ummar ƙasar na zargin gwamnati da fifita ɓangaren masu amfani da harshen Faransanci.