Sabon rikici ya barke a Sudan ta Kudu
Barkewar wani sabon rikici a Sudan ta kudu ya dakushe kimar yarjejeniyar zaman lafiyar da aka kulla tsakanin bangarorin da ke rikici a kasar, abinda ya tilastawa dimbin Yan gudun hijira tserewa zuwa Jamhuriyar Dimokiradiyar Congo domin samun mafaka.
Wallafawa ranar:
Yunkurin karbe iko da Lasu, daya daga cikin tungar Yan Tawaye na zuwa ne a dai dai lokacin da bangarorin da ke rikicin kasar ke sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a birnin Adis Ababa na Habasha wadda ake saran za ta fara aiki a karshen wannan mako.
Yan Tawayen sun sha alwashin sake kwace iko da garin wanda ya fada hannun sojojin gwammnati, matakin da ke jefa fargabar dorewar yarjejeniyar da aka sanyawa hannu.
Mai Magana da yawun Yan Tawayen SPLA, Lam Paul Gabriel yayi zargin cewar sojoji dauke da tankunan yaki da kuma muggan makamai ne suka kai hari Lasu wanda ta ke cibiyar shugaban Yan Tawaye Riek Machar.
Jami’in ya ce bangarorin biyu sun yi musayar wuta na dogon lokaci a tsakanin su.
Sai dai kakakin sojin kasar Santo Domic Chol ya yi watsi da zargin cewar su ne su ka kaddamar da harin.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu