rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Morocco

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Zanga-zangar nuna bacin rai a kasar Morocco

media
Wani yanki da ake hako gawayi Reuters

Dubban mutane ne suka gudanar da zanga-zanga a birnin Jerada da ke arewacin Morocco don nuna fushi dangane da mutuwar mutane biyu a wata mahakar ma’adinai.


A  yau litinin  da dama daga cikin masu zanga-zangar ne suka sake fitowa don gani hukumomin sun dau matakan da suka dace don kawo karshen wannan matsalla a yankin na Jerada.

Masu zanga-zangar na zargin mahukunta da nuna sakaci ta hanyar kin killace wannan tsohuwar mahakar ma’adinai da aka daina aiki a cikinta tsawon shekaru.

Kasar Morocco na daya daga cikin kasashen Afrika dake hako gawayi da kuma ke sayar da shi .