rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Liberia

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Zaben Liberia: Magoya bayan George Weah sun soma murna

media
Dan takarar shugabanci Liberia George Weah REUTERS/Thierry Gouegnon

A yayin da ake dakon fitar da sakamakon zaben shugabancin Liberia a hukumance, magoya bayan dan takarar jam’iyyar CDC, George Weah, sun soma murnar samun nasara a kan Joseph Boakai na Jam’iyyar UP mai mulki.


Murnar magoya bayan George Weah ya biyo bayan alamomin da suka ce ya nuna jagoransu na gaban Joseph Boakai wajen samun yawan kuri’u.

Tun a cikin daren jiya Magoya bayan ke aikewa junansu sakon ta ya murna ta dandalin sada zumunta, yayin da wasu ke dandazo a shalkwatan CDC da ke titin Tubman Boulevard a birnin Monrovia.

Wakilin RFI Hausa a birnin Monrovia ya rawaito cewa, mutanen da ke goyon bayan Mista Weah sun tanadi kayayyakin kade-kade da raye-raye, wanda hakan wata alamar ce, na sun shirya tsaf don gudanar da gagarumin biki da zaran an gabatar da Weah a matsayin sabon shugaban Liberia na 25.

Duk da cewa Kundin tsarin mulkin Kasar ya bada daman fitar da sakamakon zaben cikin kwanaki 18, Shugaban hukumar zaben kasar Jerome Kokoya, ya shaida wa RFI cewa, suna saran fitar da sakamakon cikin kwanaki uku zuwa hudu masu zuwa.

Cibiyar bunkasa Demokradiya ta Amurka, NDI da ta sanya ido a zaben ta bayyana cikaken gamsuwa kan yadda aka gudanar da zaben.

Tuni al'ummar kasar suka koma gudanar da harkokinsu na yau da kullum.