rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Kamaru Equatorial Guinea

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

An kama mutane dauke da makamai suna kokarin shiga Equatorial Guinee

media
Taswirar kasar Kamaru GOOGLE Maps

Yan Sandan Kamaru sun sanar da capke kusan mutane 30 dauke da makamai daf da kan iyaka da kasar Equatorial Guinee.


Jakadan kasar Equatorial Guinee a Paris Miguel Oyono Mifumu ya bayyana cewa daga cikin mutanen dake tsare yanzu haka an gano yan asalin kasashen Cadi, Afrika ta Tsakiya,Kamaru da kasar Equatorial Guinee tareda rakiyar wani Janar da aka ki bayyana kasar sa.

Equatorial Guinee kasa mai arzikin man feutr na daga cikin kasashen Afrika da Shugabanta ya jima kan karagar mulki da kuma aka yi kokarin kifar da mulkin sa a shekara ta 2004.