rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Nijar Mahamadou Issoufou

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Yan Adawa na shirin gudanar da zanga-zanga a Nijar

media
Wasu daga cikin masu zanga-zanga a Birnin Yameh na Jamhuriyar Nijar BOUREIMA HAMA / AFP

A karshen wannan makon ne yan adawa a Jamhuriyar Nijar ke shirya gudanar da zanga-zanga domin nuna rashin amincewar su da wasu daga cikin matakan da hukumomin kasar ta Nijar suka dau a baya.

Yan adawan na samun goyan bayan kungiyoyin farraren hula,wanda da da jimawa suka nuna cewa ba su amince ba da matakin da Gwamnatin ta dau.


Wannan zanga-zanga na zuwa ne a dai-dai lokacin da wani rahoton Bankin Duniya ya bayyana cewa ‘yan siyasa da rashin hukunci ya sa talauci ya karu a Nijar musamman ga mazauna karkara, abinda ke sa yawancinsu barin yankunansu zuwa birane ko wasu kasashen makwabta domin ci-rani.

Yan adawa na ci gaba da yi kira zuwa Hukumomin kasar don gani sun mutunta dokokin kasar kamar yada kudin tsarin mulki ya tsara.