rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Equatorial Guinea Tattalin Arziki Sudan Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

An dakile yunkurin juyin mulki a Equatorial Guinea

media
Fiye da shekaru 38 kenan shugaba Obiang ke jagorancin kasar mai arzikin man fetur amma kuma fiye da kaso biyu bisa ukun al’ummarta na cikin halin matsanancin talauci. AFP/JEROME LEROY

Gwamnatin Equatorial Guinea ta ce ta dakile yunkurin juyin mulkin da ake zargin masu adawa da shugaban kasar Teodoro Obiang Nguema tare da goyon bayan wasu kasahen ketare sun shirya yi. Tuni dai ma’aikatar tsaron kasar ta sanar da kame jakadan kasar a chadi wanda shima ake zargi da hannu a yunkurin juyin mulkin.


A wata sanarwa da ministan tsaron kasar Nicolas Obama Nchama ya karanto kai tsaye yau ta gidan rediyo mallakin gwamnatin kasar, ya ce an yi yunkurun juyin mulkin ne ranar 24 ga watan Disamban shekarar da ta gabata, wanda na hadin gwiwa ne tsakanin ‘yan adawa da kuma wasu kasashen ketare.

A cewar sanarwar hadakar mutanen da suka jagoranci yunkurin juyin mulkin sun hadar da ‘yan Chadi da ‘yan Sudan da kuma ‘yan jamhuriyyar Afrika ta tsakiya wadanda aka tsara za su kai hari fadar shugaba Teodoro Obiang a lokacin hutun karshen shekara.

Nicolas Obama ya ce ya ce jami’an tsaronsu da taimakon hukumar tsaron kamaru sun yi nasarar dakile juyin mulki inda kuma suka kame da dama da ake zarginsu da hannu ciki.

Sanarwar dai na zuwa ne bayan kamaru ta sanar da kame wasu tarin mayaka dauke da muggan makamai akan iyakar kasar ta Equtorial Guinea ranar 27 ga watan Disamba.

Fiye da shekaru 38 kenan shugaba Obiang ke jagorancin kasar mai arzikin man fetur amma kuma fiye da kaso biyu bisa ukun al’ummarta na cikin halin matsanancin talauci.