Isa ga babban shafi
Habasha

Gwamnatin Habasha zata saki dubban fursunonin siyasa

Gwamnatin Habasha ta yi alkawarin sakin wasu fursunonin siyasa tare da kulle gidan yarin Maekelawi da ake ajje fursunonin a baya.

Firaministan kasar Habasha, Hailemariam Desalegn.
Firaministan kasar Habasha, Hailemariam Desalegn. REUTERS/Tiksa Negeri
Talla

Kungiyoyin kare hakkin dan adam sun dade suna zargin cewa gwamnati tana amfani da gidan yarin na Maekelawi da ke birnin Addis Ababa ne a matsayin sansani na take hakkin dan adam.

Alkawarin da Firaminista Hailemariam Desalegn ya yi, ya zo a yanayi na bazata, ganin cewa a baya gwamnatinsa tana kare kanta da cewa, tana daukar tsauraran matakai na kame mutanen da dama ne, domin sha’anin tsaro, matakin da masu fafutuka ke ganin hanya ce kawai da take bi wajen murkushe ‘yan adawa.

Firaminista Desalegnya ce gwamnatinsa ta yanke shawarar yin afuwar ce domin tabbatar da hadin kan kasa da kuma dorewar dimkokaradiyya.

Kungiyar kare hakkin dan adam ta Amnesty International ta yi maraba da matakin na Hailemariam, inda ta ce lokaci yayi da za a kawo karshen cin zarafi da kuma keta hakkin al’umma da sunan fursunonin siyasa.

A baya kungiyar Amnesty tana daga cikin kungiyoyin kare hakkin bil’adama da suka yi kaurin suna wajen sukar gwamnatin Habasha, musamman kan yadda ta ke fakewa da cibiyar ta Maekelawi wajen garkame ‘yan adawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.