Isa ga babban shafi
Libya

Ƴan-cirani 25 sun nutse a teku

Ƴan-cirani masu niyyar tsallakawa Turai aƙalla guda 25 ake tunanin sun halaka sa’ilin da kwale-kwalen da suke ciki mai ɗauke da mutane kimanin 150 ya nutse a yankin ruwan Libya.

Bakin-haure masu son tsallaka kogin Mediterranian daga Libya zuwa Turai.
Bakin-haure masu son tsallaka kogin Mediterranian daga Libya zuwa Turai. Patrick Bar / SOS Méditerranée
Talla

Masu gadin teku na Jamus 'Sea Watch', suka bayyana labarin a shafinsu na twitter, inda suka ce har yanzu ba za a iya tabbatar da adadin waɗanda abin ya rutsa da su ba.

Masu gadin gaɓar teku na Italiya sun ce an samu nasarar ceto mutane 85 daga cikin waɗanda kwale-kwalen ya nutse da su.

Wannan ne karo na farko da aka samu nutsewar kwale-kwalen da ke ɗauke da bakin-hauren, duk da dai akwai yiwuwar waɗansu kwale-kwalen za su iya nutsewa ko ma sun nutse ba tare da an gano hakan ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.