rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Tarayyar Turai Kenya Uhuru Kenyatta Raila Odinga

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Cacar-baki ta kaure game da sakamakon zaɓen Kenya

media
Masu zanga-zanga a kasar Kenya. REUTERS/Thomas Mukoya

Sama da mutane 90 ne suka mutu a tashin-tashinar da ke da alaƙa da zaɓen, inda aka zargi ƴansandan ƙasar ta Kenya da aikata akasarin kashe-kashen.


Ƙungiyar tarrayar Turai ta bakin shugaban tawagar masu sa ido a zaɓen na Kenya Marietje Schake, ta bayyana zaɓen shugabancin ƙasar da ya gabata a matsayin zaɓen da ke cike da kura-karai.

Rahoton wanda aka fitar a Brussels na ƙasar Belgium a maimakon ƙasar ta Kenya, ya yi kakkausar suka a kan sakamakon zaɓen.

Sai dai ƙasar ta Kenya ta bakin Jakadanta da ke Belgium, Johnson Weru, ta la’anci sanarwar daga masu sa ido a zaɓen, tare da cewa hakan na iya haifar da rikici a ƙasar.