rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Najeriya Noma

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Gwamnatin Najeriya za ta janyo hankulan al’ummar kasar zuwa aikin gona

media
Yankin da ake noman Shinkafa ISSOUF SANOGO / AFP

Daya daga cikin muhimman matakan da gwamnatin Muhammadu Buhari ta dauka don janyo hankulan al’ummar kasar zuwa ga aikin gona shi ne hana shigo da kayyakin abinci daga ketare.

Daukar matakin dake zuwa a dai-dai lokacin da ake fuskantar  rikici tsakanin manoma da makiyaya a wasu yankunan kasar.


Wasu daga cikin yan kasar na ganin cewa kafin daukar irin wannan mataki, kamata ya yi ta inganta bangaren aikin gona da kuma samar wa manoma abubuwan da suke bukata.

Idan aka yi tuni a yan watanni da suka gabata gwamnatin Najeriya ta umurci jami’an Kwastam da su mayar da hankali zuwa kayakin abinci da ake shigo da su kasar.