Isa ga babban shafi
Jamhuriyar Congo

Sojin Jamhuriyar Congo sun kaddamar da farmaki kan 'yan tawaye

Rundunar sojin Jamhuriyar Congo, ta kaddamar da farmaki kan kungiyar mayakan ‘yan tawayen Uganda ta ADF a birnin Beni da ke gabashin kasar.

Jami'an sojin Jamhuriyar Congo a yayinda suke tunkarar birnin Goma da ke gabashin kasar.
Jami'an sojin Jamhuriyar Congo a yayinda suke tunkarar birnin Goma da ke gabashin kasar. REUTERS/Kenny Katombe
Talla

Sojojin Jamhuriyar Congon sun kaddamar da farmakin ne tare da hadin gwiwar takwarorinsu na Uganda, wata guda bayan da aka kai wa dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya hari, tare da hallaka 15 daga ciki a watan Disamba da ya gabata, harin da ake kyautata zaton ‘yan tawayen na ADF ne suka kai.

Akalla sojojin Jamhuriyar Congo 5 ne suka hallaka, yayin da kuma harin na kungiyar mayakan na ADF ya jikkata wasu sojojin 53.

Kawamandan sojin Jamhuriyar Congo da ke lura da lardin Kivu, Janar Marcel Mbangu, ya ce suna sa ran gagarumin farmakin ya zama na karshe, har sai sun kwace dukkanin yankunan da suke karkashin ‘yan tawayen.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.