rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Libya Rikicin Kasar Libya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Rikici ya hallaka mutane 9 a filin jirgin saman Libya

media
Akwai dai mutum 32 da suka jikkata sai dai babu tabbacin ko sun hada da fararen hula da mayakan. Reuters

Rahotanni daga Libya sunce an hallaka mutane 9 a wani kazamin rikici da ya barke a birnin Tripoli, lamarin da yakai ga dakatarwa da kuma rufe tashar jiragen saman Mitiga zuwa wani lokaci.


Jami’an tsaro sun shaida cewa rikicin ya fara ne lokacin da ‘yan tawayen Burga suka kai wa dakarun tsaro hari da niyar kwato fursunoninsu da ake tsare da su.

Akwai dai mutum 32 da suka jikkata sai dai babu tabbacin ko sun hada da fararen hula da mayakan.

‘Yan tawayen Burga da Basheer al-Burga ke jagoranta na nuna adawarsu ga gwamnatin hadin-kan kasar da su ke zargi da aikata kisan gilla.