Somalia
Rabin al'ummar Somalia na fuskantar bala'in fari
Majalisar Dinkin Duniya ta ce sama da rabin al’ummar kasar Somalia suna matukar bukatar agajin gaggawa saboda matsalar fari, da kuma kazamin tashin hankali da ya mamaye kasar.
Wallafawa ranar:
Talla
Miliyoyin mutane ne dai suka tsere daga gidajensu, yayin da dubban kananan yara ke fama da cutuka masu alaka da yunwa.
A cewar Majalisar Dinkin Duniya, mummunan yanayin da al’ummar kasar ta Somalia ke ciki, zai kara kazanta, muddin ba’a samar da dalar Amurka biliyan 6 domin tallafa musu ba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu