Isa ga babban shafi
Cote D'Ivoire

Tsohon ministan tsaron Cote d'Ivoire zai yi zaman yari na shekaru 15

Wata Kotu da ke zamanta a Abdijan babban birnin Cote d'Ivoire ta yanke wa tsohon Ministan Tsaron kasar na zamanin mulkin Laurent Gbagbo, wato Moise Lida Kouassi, hukuncin daurin shekaru 15 a gidan yari. Da ta ke zartas da hukuncin Kotun ta ce ta samu Moise Lida Kouassi dumu-dumu da hannu a kokarin hambarar gwamnatin Alassane Ouattara.

tsohon shugaban Cote d'Ivoire Laurent Gbagbo
tsohon shugaban Cote d'Ivoire Laurent Gbagbo Issouf Sanogo/AFP
Talla

A watan Yunin shekarar 2012 ne aka kame Koise Kouassi a kasar Togo inda ya ke gudun hijira, daga bisani kuma aka mika wa gwamnatin Cote d'Ivoire.

Tun bayan mika Moise ne ake ci gaba da tabka kan rawar da ya taka wajen ganin an hambarar da gwamnatin Alassane Ouattara.

Akalla mutane dubu 3 ne suka mutu a rikicin kasar da aka shafe fiye da watanni uku ana tafkawa wanda ya samo asali daga kin amincewa da shan kayen da tsohon shugaba Laurent Gbagbo ya yi.

A farkon shekarar 2011 ne kuma dakarun Faransa da na Majalisar dinkin Duniya suka kame shugaban kasar na waccan lokacin Laurent Gbagbo tare da mika shi zuwa kotun ICC, don yi masa hukunci.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.