rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Najeriya Lafiya Kogi Cutar Lassa

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

An samu bullar cutar Lassa a Najeriya

media
Cutar wadda wani nau'in Bera ke haddasawa, masana sun ce alamunta basa wuce zazzabi mai zafi, kasala dama ciwon kai. barbaric.com

An samu bullar cutar Lassa wadda wani nau’in bera ke yadawa a jihar Kogi da ke arewacin Najeriya, bayanda likitoci suka gudanar da gwaje-gwaje kan wani mara lafiya a safiyar yau Asabar.Tuni dai Jihar ta fara daukar matakan ganin cewa cutar ta Lassa ba ta watsu zuwa wasu sassa ba.


Cibiyar da ke kula da cutuka masu yaduwa ta kasar reshen jihar kogi ta tabbatar da samun bullar cutar, inda ta ce cibiyar da hadin gwaiwar takwarorinta na sassan kasar sun gudanar da bincike tare da gano cewa tabbas marar lafiyan na fama da citar ta Lassa.

Tuni dai likitan da ya fara karbar marar lafiyar a asibitin ya fara karbar kulawar gaggawa don kare kansa daga kamuwa da cutar.

A cewar cibiyar tuni aka sanar da hukumar lafiya ta duniya WHO da ma’aikatar lafiya ta Najeriyar dama dukkanin masu ruwa da tsaki don daukar matakan da suka dace.

Haka zalika Dr Alabi babban likita a cibiyar ta Kogi, ya ce suna ci gaba da bincike tare da bin diddigin gano daga inda cutar ta faro, don tabbatar da babu sauran masu dauke da ita da ke ci gaba da rayuwa cikin jama’a.

Ya kuma tabbatar da cewa, sun fara daukar matakan wayar da kai tun bayan gano bullar cutar a safiyar yau wajen ganin ba a samu yaduwar ta ba.

Tsawon kusan shekaru biyu kenan Najeriya na fama da matsalar bullar cutar ta Lassa wadda bera ke haddasawa a sassan daban-daban na kasar, lamarin da alokuta da dama kan haddasa asarar rayuka.