rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Masar Abdel Fattah al-Sisi

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

An samu dan takaran da zai kalubalanci Al-sisi a Masar

media
Shugaban Jam'iyyar Ghad Moussa Moustafa Moussa ya kasance dan takarar da zai kalubalanci Al-sisi a zaben Maris REUTERS/Mohamed Abd El Ghany

Wani dan siyasa a Masar Mousa Mostafa Mousa ya kasance dan takara na biyu da aka tantance domin shiga zaben shugabancin kasar in da zai fafata da shugaba mai-ci Abdel Fattah al-Sisi.


Mousa ya kasance dan takara ne a dai-dai lokacin da ake ganin Al-sisi zai iya kasancewa dan takarar daya tilo lura da cewa wa’adin da aka bai wa ‘yan takarar domin bayyanan matsayinsu na gab da cika.

Mousa da ya ke jagorantar jam’iyyar Ghad party, ya kasance dan takaran ne bayan samun adadin mambobin da ake bukata kafin a karbi takardan shedar takarar.

A ranar lahadi da ta gabata ne dai ‘yan takarar da dama da ke jagorancin Jam’iyyun adawa suka sanar da cewa za su kauracewa zaben da ake shirin gudanarwa a watan Maris mai zuwa, bayan bayyana cewa shugaban kasar Al-sisi na son amfani da karfi wajen gani ya sake komawa mulki.

Kazalika jam’iyyun na zargi al-sisi da kalubalantar manyan ‘yan adawa da kuma aike wasu gidan kaso.

Al-sisi dai tsohon kwamandan sojin kasar Masar ne da ya jagoranci kifar da gwamnatin Mohamed Mursi, a shekara ta 2014, wanda hakan ya ba shi daman hawan karagar mulkin kasar.

Kazalika ana saran shugaban ya sake samun nasara a wannan karon cikin sauki, wadda shi ne karo na uku tun bayan zanga-zangar shekara ta 2011 da ta hambarar da shugabancin Hosni Mubarak da ya shafe shekaru da dama a karagar mulkin kasar.