rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Tarayyar Afrika

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Tsarin fasalta siyasar Afrika ta bangaren tsaro da yaki da cin hanci

media
Antonio Guterres, Sakatary Majalisar Dinkin Duniya RFI/Richard Riffonneau

Yau litinin Shugabannin kasashen Afirka ke ci gaba da taron su a Addis Ababa, inda ake saran zasu mayar da hankali kan shirin yaki da cin hanci da rashawa.

Tuni kungiyar ta bayyana nada shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari a matsayin wanda zai jagoranci yakin, kuma shi ake saran ya jagoranci zaman taron na yau.


A daya bangaren Sakatary Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya bayyana damuwar sa gani kalubale da  dakarun wanzar da zaman lahiya ke fuskanta a Nahiyar Afrika wajen gudanar da ayyukan su.

Guterres ya bukaci kasashen Afrika su bayar da hadin kai a kokarin su na yakar kungiyoyin dake dauke da makamai. Lamarin dake kawo koma baya ga kokarin majalisar Dinkin Duniya na  wanzar da zaman lahiya a yankin.