rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Najeriya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Amnesty internationnal ta yi kira zuwa Gwamnatin Najeriya

media
Makiyaya a kan hanyar su a wani kauye Getty Images/ Aldo Pavan

Kungiyar kare Hakkin Bil Adama ta Amnesty International ta bukaci gwamnatin Najeriya ta tashi tsaye domin kawo karshen kashe kashen da ake samu sakamakon rikici tsakanin manoma da makiyaya.


Daraktar kungiyar a Najeriya, Osai Ojigho ta ce a cikin watan Janairu kawai an kashe mutane 168 a rikice rikicen da aka samu a Jihohin Adamawa da Benue da Taraba da Ondo da kuma Kaduna, yayin da gwamnati ta gaza wajen kare rayukan jama’a.

Daraktar ta ce wasu lokuta jami’an tsaro kan yi amfanin da karfin da ya wuce kima wajen kashe mutane maimakon shawo kan rikicin, kana kuma ba’a hukunta masu aikata laifufuka.