rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Kenya Raila Odinga Uhuru Kenyatta

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Kenya:Raila Odinga ya rantsar da Kansa

media
Madugun adawar kenya Raila Odinga lokacin da ya ke rantsar da kansa a birnin Nairobi REUTERS/Baz Ratner

Rahotanni daga birnin Nairobi na cewa madugun adawa kasar Kenya, Raila Odinga ya rantsar da kansa a matsayin sabon shugaban kasa a gaban dafifin jama’a.


Wannan kasaitaccen bikin rantsuwa anyi shine a fitaccen dandalin tunawa da Uhuru da ke Nairobi, kuma duka-duka a cikin minti 10 aka kammala.

Magoya bayan Odinga dai sun ce shine wanda ya lashe zaben kasar ba shugaba mai ci Uhuru Kenyata ba.

A watan Agustan shekarar da ta gabata Kotun kolin kasar ta soke zaben da ya bai wa Shugaba mai-ci Uhuru Kenyatta nasara kan dalilan magudi.

Sai dai kuma da aka sake yin zaben zagaye na biyu wanda ‘yan adawa suka kauracewa Kenyatta ya sake samun nasara a watan Nuwamba 2017.

Daga cikin dalilan kauracewa zaben da ‘yan adawan suka gabatar akwai zargin kin aiwatar da wasu sauye-sauye a hukumar zaben kasar.

A yanzu dai Raila Odinga na nuna babu gudu ba ja da baya a game da matakin da ya dauka.