rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Tarayyar Afrika Tattalin Arziki

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Soma amfani da tsarin sufurin jiragen sama na bai-daya a Afrika

media
Wani jirgin sama malakin Max Air a Nijar Wikip├ędia

Kungiyar Tarayyar Afirka ta sanar da fara amfani da tsarin sufurin jiragen sama na bai-daya a tsakanin kasashen nahiyar, bayan da kasashe 23 suka sanya hannu kan yarjejeniyar da ke tabbatar da haka a birnin Adis Ababa na kasar Habasha.


Yarjejeniyar na daya daga cikin abubuwan da kungiyar ta Tarayyar Afirka ta jima tana fatan ganin ta tabbata, wannan kuwa da zummar kawo sauki ga zirga-zirgar jiragen sama a tsakanin kasashen nahiyar.

Sabon shugaban kungiyar tarayyar Afirka sannan shugaban Rwanda Paul Kagame, da kuma shugaban hukumar kungiyar ta AU Moussa Faki Mahamat, sun bayyana yarjejeniyar a matsayin wadda za ta ingata sha’anin sufuri a nahiyar wadda sauran nahiyoyin duniya suka yi wa fintinkau a fagen sufurin jiragen sama.

Wasu daga cikin manyan manufofin da ake fatan yarjejeniya za ta samar, sun hada da kara adadin matafiya a jiragen sama, tabbatar da cewa a duk inda matafiyi zai je a Afirka, to akwai jirgin da zai dauke shi, sannan kuma da rage farashin tikiti ga matafiya.

Wani bincike da bankin duniya ya gudanar a shekara ta 2010, ya nuna cewa mafi yawan kasashen Afirka na takaita zirga-zirgar a tsakaninsu ne domin kare kasuwar kamfanonin jirage mallakinsu, to sai dai matakin na kawo cikas ga cigaban tattalin arzikin nahiyar a cewar bankin na duniya.