rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Liberia

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Shugaba George Weah ya sha alwashin samar da sauye-sauye

media
George Weah,Shugaban Liberia REUTERS/Thierry Gouegnon

Shugaban kasar Liberia George Weah ya sha alwashin samar da wasu sauye-sauye a kundin tsarin mulkin kasar, musamman kan dokokin da ke nuna wariya ko bambancin launin fata.


Haka zalika shugaban ya kuma yi alkawarin karbar rage albashinsa, inda ya ce kasar za ta rika amfana da kaso 25 cikin dari na albashin sa, sakamakon halin da kasar ke ciki na karancin kudi da faduwar tattalin arziki.