rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Najeriya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Za a soma taron lalubo hanyar magance rikicin Fulani da manoma

media
Wani Makiyayi na kiyon dabbobinsa a kusa da wata gona Faceboock

Majalisar Dattawan Najeriya ta bayyana shirin fara wani taron hadin gwuiwa tare da fadar shugaban kasa domin lalubo hanyar magance rikicin Fulani makiyaya da manoma.


Gwamatin Najeriya ta ƙaddamar da wani shiri a baya na lalubo hanyar magance tashin hankalin da ke haddasa asarar rayuka tsakanin Fulani makiyaya da manoma a ƙasar.

Mai Magana da yawun mataimakin shugaban ƙasar Laolu Akande ya ce, Farfesa Yemi Osibanjo ya gana da wasu manyan Sarakunan arewacin ƙasar da suka haɗa da Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II da Lamidon Adamawa Muhammad Barkindo Mustapha kan yadda za a kawo karshen wannan rikici.

Baba Ngelzerma, Sakataren kungiyar Fulani ta Myetti Allah da ya halarci taron n, ya shaida wa sashen hausa na RFI cewa, baya ga batun rikicin Fulani da makiya, tattaunawarsu ta kuma mayar da hankali kan yadda za a samar da zaman lafiya mai ɗorewa a Najeriya